AMINA yarinyace da ta taso cikin fuskantar ƘALUBALEN RAYUWA daban daban tun daga ranar da tazo duniya har girmanta,Ta taso bata san waye mahaifinta ba,mahaifiyarta ta kasance tana ɗauke da cutar hauka,TASHA itace gidansu a nan suke kwana suke tashi,ruwa, iska, zafi,sanyi duk tsananin su a kansu yake ƙarewa,ta haɗu da saurayi wanda yake ba musulmi ba watau Christian inda suka ƙulla soyayya,saidai mahaifiyar shi wadda ta kasance tana sana'ar sayar da abinci a TASHAR da su Meenal suke rayuwa tayi tsalle ta dire ta shiga ta fita ta lalata alaƙar dake tsakanin ɗanta Samuel da kuma Meenal. A cikin wannan halin rana ɗaya aka wayi gari Meenal tana ɗauke da juna biyu a lokacin shekarunta duka duka goma sha biyar a duniya.
4 parts