In ya kalli FA"IZA sai yaji Fiye da madaukacin Takaicin daya ke ji in ya tuna itace yau MATAR SA..Fa"iza ba mafarkin sa bace a irin Rayuwar ISHAQ KABIR KAROFI..Sam Fa"iza bata dace ko kada'n da Tsarin Rayuwarsa ba, kowa yasan Ishaq dan gayu ne mai ilimi ne,kyakyawa ne dan Fafane dan Alfahari ne Duniya tasan da zamansa mai Burin Auran mace FARA mai kyau mai Tarin kwalayen matakan karatun.Zamani SAI DAI KASH"
Hakan bai samu ba..Sakamakon kutse da Fa"iza tayi cikin Rayuwarsa ta Ruguza Mafarkinsa har Abada bazai daina Hango FA"IZA a matsayin Nakasun Mafarkinsa ba..