FANSAR FATALWA! Labarin FANSAR FATALWA labari ne da ya ƙunshi cin amana tsantsa wanda ƙawaye suke yiwa junan su. Labari ne akan wasu ƴan mata guda biyar waɗanda suka taso cikin wata irin azababiyyar aminta,wadda idan aka tashi kwatancen aminan ƙwarai su ake fara kawowa a sahun farko,sai dai kash! Duk da irin wannan aminta ta su hakan bai hana su cin amanar juna ba,inda suka haɗa kai suka ci amanar ɗaya daga cikin su wadda sanadiyyar haka ta rasa duk wani farin ciki na rayuwa,kama daga kan ahalin ta,karatun ta,saurayin ta wanda zata aura,at long last tazo ta rasa rayuwar ta,sai dai kuma ashe hakan da suka aikata basu san cewa reshe ne zai juye da mujiya ba.Taci alwashin ƊAUKAR FANSA sai dai ta yaya hakan zata kasance?Ta wace hanya zata bi ta rama wannan cutarwar da aminan ta suka mata?domin ance Rama cuta ga macuci ibada ne. Hmmm akwai ƙura fa a cikin wannan labain ina faɗa muku tafiyar ta musamman ce,amma fa sai wanda ya biyo ni,saboda haka ma yasa na rubuta shi a matsayin Free book saboda Irin darussan ciki.