Ashraf saurayi ne ɗan shekara 31. Yana da kyau da kwarjini da high sense of fashion. In dai kyakykyawar mace ce to Ashraf zai bita, sai dai kuma idan matar aure ce to ta riga ta zama masa forbidden fruit. "Bana taɓa kayan wani" mantra ɗinsa kenan.
Lokacin da Zainab Qayyisah ta zo bautar ƙasa bata cikin irin 'yanmatan da yake bibiya. Ta mishi guntuwa, ba ta da gaba da bayan da zai ja hankalinsa.
Sai dai kafin ya ankara wannan 'yar ficilar, wannan PEANUT ɗin ta shiga rayuwarsa, ta shiga jinin jikinsa ta ɗaure jijiyonsa ta hana zuciyar sakat.
A kowanni lokaci zai zaɓi PEANUT ɗinsa saboda saboda saboda...
Ku karanta ku sha labari.
©AzizatHamza2023...All Rights Reserved