Tausayi da kuma taimako ya sa shi jajiɓota ya kawota cikin danginsa na Fulanin usul. Ta zauna cikin tsangwama da ƙyashi.
To kasancewarsu mabiya addini da kuma yare mabanbanta hakan bai hana soyayya mai sanyi ƙawalniya a zuciyarsu ba. Sai dai soyayyarsu ta zo da jarrabawa kala-kala. Wannan jarrabawa kuwa bai tsaya iya su ba, sai daya ya shafi 'yarsu Zaytoonah...
Cikin wannan tafiya zaku ga yadda ake SO da zuciya ɗaya. SO da baya tsufa. SO daya ke jure duk wani juyi-juyi na rayuwa.
SO ɗaya ne tak. Kuma Maryam Nkiru ta yiwa TJ shi. Duk rintsi, duk wuya soyayyarta na TJ ne.
Ku biyoni a labarin Chronicles of Zaytoonah dan samun labarin soyayya da kuma halin rayuwa...