Ban cire rai ba, ban kuma yarda zuciyata ta karaya ba, kowanne ɗan Adam da kalar ƙalubalen da yake fuskanta a rayuwarsa. Soyayya! Soyayya!! wannan halitta ita ce ƙaddara ta, ita ce ke shirin wargaza ɗan ƙaramin mafarki na, sam ba ta yi min adalci ba, bata ɗauke ni ta ijeye a ɓigiren da ya dace ba. Ina matuƙar jin ciwo, ina cutuwa, ina zubar da hawaye sau ba adadi a duk lokacin da na kalli rayuwata da inda ƙaddarata ta jefa ni.All Rights Reserved