MACE CE KUMA BAHAUSHIYA CE! "Kasancewar hakan bazai canza cewa itama mutum ce kaman kowa ba." "bai kuma isa sawa a hana mata 'yanci kaman kowa ba." "sannan kuma hakan bai isa zama dalilin da zaisa a kyamaceta ba." "Bai kuma isa hana mata "kujerar fada aji" a alumma ba." "Itama kaman kowa take" "kada wasu dalilai marasa tushe su sa ayi mata kallon bata isa ba" ********** MACE CE!! "YA CE! MATA CE! UWA CE! Ba BAIWA bace. ********** "ke baki isa ki bani shawara in dauka ba wallahi kinyi kadan Rabi!" Malam Ya'u ya fada cikin 'karaji da tada jijiyoyin wuya. cikin rashin tsammani kaman daga sama ya ji Indon tace "Meyasa" baki bude yake kallonta, bawai da karfi tayi maganar ba,asalima tayita a nutsen da sai kana kusa sosai zakajita. Mamakinshi bai wuci yanda tayi maganar kaitsaye ba babu wani alamun tsoro. "saboda ke MACE ce karamar kwakwalwa ce daku!" ya fada a dake. kaman saukar aradu haka maganar tazo mata. "Tabbas yau sai ta tabbatar mashi cewa MACE ta isa itama" Ta fada a zuciyarta kafin ta bude baki tace.... ******* #Boddozee #BAHAUSHIYA