16 parts Complete A masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa.
Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta!
DEEN ya zama wani bangare na rayuwar ABIEY da ZAHRA, ya sabunta wasu shafukan na rayuwarsa da ta su, ya kuma jefar da wasu.
A yayinya da ra'ayoyin juna ya fara girmama, sai tafiyar ta sauya salo, dogon zaren ya tsinke. Tabbas rayuwa bata da sauki ga mutanen da soyayyah ta auresu. Sai dai shagaltuwa ya saka zuciyoyinsu yin wasi-wasi. CIWON - SO labari ne da aka gina akan wata irin soyayya mai ratsa jini da zuciya.