19 parts Ongoing "Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi...
Daga lokacin da na fahimci haka, sai tsoro da fargabar me zai faru a gaba ya fice a zuciyarta. Tafiyar da babu dawowa ta zama dakuna..."
TA ƘI ZAMAN AURE...
Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da daure kai. Wata kalar kaddara ce mai rikitarwa, shimfida ce dake lalaye tafiyar wasu daidaikun mata....
Tafiya ce ta irin matan da duniya ta canja musu zane, suke da wani rufaffen sirri a zuciya! Sai dai kadan daga masu ilmi ke fahimta. A cikin rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa shim kun ankara da haka?
Mabudin kowace kofa makulli ne sai dai wannan kofar a balleta ne ta kasa, sai shigar cikinta ta kasa yi ma mai dakin dadi.
Al'umma sun kasa yi mata uzuri iyayenta sun kasa fahimta, mazajen kuma sun kasa riko...? Uba na gari jigo, sai dai ita bata dace ba, miji na gari gimshiki a nan din ma dai bata dace ba, kuma duka laifin yana komawa zuwa gareta ne.... Duniya ta yi mata juyin masa, ta yadda ta kasa banbance fari da baki, ji da gani sun mata nisa, albishin daya take jira... mutuwa...!