Fathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA.
FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwatsam tariski kanta da zamowa uwar ƴaƴa kuma abokiyar rayuwa ga MAHMOUD na har abada. Kar ku manta su ɗin abokan juna ne kuma aminan juna, shin taya hakan zai faru? Ku biyo mu a wannan littafi namu mai suna FATHIYYA don warwarewar zare da kuma abawa, daga taskar UMM ASGHAR da kuma BILLY S FARI.