12 parts Ongoing *A lokacin da doka, ke ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci, ko ta halin ƙaƙa, an samu naƙasu a sanadiyyar bara gurbi, da masu yi wa dokar bi ta da ƙulli. Nasara na daf da samuwa, soyayya ta yi kutse, wurin gwamutsa ƙaddarori biyu wuri guda. Ga soyayya da ta'addanci ga kuma doka, ko wane ɓangare ne mai gaskiya? Waye zai yadda ya bi wani *ƘARFE A WUTA ka fi ƙarfin ɗauka da hannu....ƘARFE A WUTA sai dai kallo. Ƴar kasada ce, kuma mai kishin ƙasa a zatonta komai zai zo da sauƙi, kamar yadda take hangensa, sai dai ƙaddara ta shammace ta, abun harinta ya zama abun bawa kariyarta*