AUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨
Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra) wadda tasha wahalar rayuwa ita da kannenta wajen marikin su kuma babban wa a gurin mahaifinsu, inda ta samu scholarship din karatu zuwa dubai.
Amar hamshakin mai kudi ne wanda mahaifinshi Alhaji taura ya bar mashi gado dukda bai damu da dukiyar Tashi ba saboda burinshi na zama babban general army officer a United arab, Amar is a definition of charming, wealthy, handsome and filthy rich guy, babu abunda bashi dashi a duniya saidai ance mutun Tara yake bai cika goma ba, yana fama da cutar oligospermia (rashin kwayayen haihuwa da yawa) inda likita ya shaida mashi chance daya yake dashi na haihuwa idan ya rasa bazai taba haihuwa ba, wannan yasa dole aure ya shigo cikin plans dinshi na rayuwa wanda kwata kwata ada bashi da burin haka.
Amra ta shugo rayuwar shi lokaci guda babu zato babu tsammani inda sanadiyar auren yarjejeniyar da sukayi akan ta samu katin kasa a karkashin sa zai bayyanar da wani babban sirrin dake boye shekaru da suka wuce....
Littafine wanda zai ilimantar kuma ya nishadantar sannan zai tabo al'adu daban daban da rayuwar data banbanta da kasarmu ta hausa...❤️😻
Pure loveeeeeee!!!🙈🔞
Hausa-English novel📝Todos los derechos reservados