Sun mai da ZINA kamar ado a cikin al'umma, matar aure wacce ta wofintar da auranta take aikata ZINA da mak'ocinta har suka haifu, d'aya kuma tana amfani da aikin da take yi tana zuwa hotel-hotel tana aikata ZINA. ZALIHA yarinya ce mai ilimi wacce gaba d'aya unguwar su suke mata lak'abi da ZATUDDEEN (Ma'abociya addini) saboda tsantsan kamun kanta. Sai dai ita ma a bayan fage tana aikata sharholiyanta da mijin y'arta wacce ta fifita aiki akan kula da mijinta.All Rights Reserved