Izza, mulki, k'asaita sun tattara a gare ta ita kad'ai. Y'ar sarki ce, jikar sarki, matar sarki. Bata k'aunar talaka bata son had'a hanya da talauci, burin ta d'aya tak ya rage a duniya shi ne d'an ta ya zama sarki ta zama babar sarki kuma kakar sarki ta gobe; Sai dai kash! Y'ay'anta maza har guda uku masu matuk'ar kama da juna sun kasance babu wanda yake da qualities d'in rik'e ragamar Al'umma. Na farko shaye-shaye, na biyu kurma ne, na uku ba ya da lafiyar k'wak'walwa. A Lokacin da burinta ke gab da cika kwatsam Y'ar talakawa, bak'a, gurguwa mai tallan abinci ta shigo rayuwar samarin 'ya'yan nata guda biyu, gurgurwar da ta zama silar girgizawar duniyarta da burinta, gurgurwar da ta haddasa mata raunin da bata da shi, gurguwar da ta zamar mata inuwar dodo...shin me zai faru? Ta wacce hanya gurguwa ta kutso cikin rayuwar wad'annan sarakunan...? Waye zai zama sarki cikin su ukun duk da kasnacewar su masu kama d'aya......? ina alwashin da ta ɗauka na ganin cewar sai taga bayan duk wanda ya nemi ya ruguza lissafinta?, ina alwashinta na cewar sai ta kassara rayuwar wanda ya kawo kutsen hana ɗanta zama sarkin gari....? Zai cika ko A'a?.
*KWANTAN ƁAUNA*
Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)
33 parts Complete
33 parts
Complete
Labari akan wata uwar miji wacce ta takurawa matar dan ta tin kan suyi aure. Komai ta tashi ta turo mata but sai ya kare akan ta. Shin uwar mijin na gane gaskiya ko kuwa? Mushiga ciki dan jin me ke akwai.