Murya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina".
Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito daga cikin kicin dinta da yake falon.
Take na tuna dangantakarsa da Baba ta Bulkachuwa. Wani irin tashin hankali ya sake ziyarta ta. Kunya da ki'dima suka rifar mini, na rasa yadda inda zan tsoma raina.
Na kalle shi, na ga alamun damuwa a tare da shi, haka da na kalli Babar sai na ga ita ma tana cikin zullumi.
Kunyar yadda na zo gabanta ina fa'din bana son dan cikinta ta nemi zautar da ni, domin bansan ya aka yi ba na zabura na tsallake kwanukan abinci da na ruwa na yi waje a guje.
Ina jinta ta biyo ni tana fa'din Yabi! Yabi!".