Story cover for SOFIA ✔ by DielaIbrahim
SOFIA ✔
  • WpView
    Reads 569
  • WpVote
    Votes 43
  • WpPart
    Parts 24
  • WpHistory
    Time 4h 16m
  • WpView
    Reads 569
  • WpVote
    Votes 43
  • WpPart
    Parts 24
  • WpHistory
    Time 4h 16m
Ongoing, First published Sep 24, 2023
Nakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE  da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sila ne ta dalilin Depression a turance kenan, to amma likitoci sun faɗa cewa da ace mahaifiyar bata da ciki da ita zata samu rauni (na rashin ji, ko kuma rashin gani, ko ciwon hauka) sai akayi rashin sa'a uwar na ɗauke da juna biyu sai abin ya sauka akan abin da ke cikin ta,Maimakon yayi ma uwar illah sai yayi ma SOFIA illah aka haife ta nakasasshiya kuma likitoci sun tabbatar ba lallai ta iya tafiya ba saboda jijiyoyin da zasu taimake ta wajan tafiya sun mutu basu da karfin da zasu iya zama lafiyayyun jijiyoyi.

Shin da gaske ita ɗin MABARACIYA ce?,  Yaya zata kalli AL'UMMA ko yaya AL'UMMA zasu kalle ta?, SADAUKARWA mai cike da rugujewar Mafarkai da Burika, SARƘAƘIYA, KADDARA, RAYUWA mai cike da ZAGON ƘASA.
All Rights Reserved
Sign up to add SOFIA ✔ to your library and receive updates
or
#91partner
Content Guidelines
You may also like
NANATOOU (DIYAR KAKA) by AishaMaaruf1
20 parts Ongoing
Labari ne akan wata Yar kauye da aka sangarta ta, Duk kauyen su ta addabi kowa ba mai iya tsawata mata, tun daga yara, matasa, yan mata, tsoffi, hatta da sarkin garin duk ta addabe su........................ wani matshin saurayi da baze wuce shekara sha takwas ba ya ce"ya ana miki magana kin miyar da mutane yan iska". kallan Shi tayi Sama da kasa tana gyara dan kwalin ta sai wani murgude murgude take ta ce"ba yan iska ba karuwai da kwartaye na mai da ku ko kuma ka ce yan goguwa ta fada tana murgude baki tare da hararar shi". Keh ni za kiwa rashin kunya, ganin yanda ya harzuka yasa ta ja da baya tana shirin ko ta kwana, dan ubanki ni zaki zaga, ja da baya ta yi ta tattare zanin ta ta ce" ba dai ubana ba sai dai ubanka mln salisu mai wankin hula". Toh wallahi ubanki zan ci idan na kama ki, sai na karya kasusuwan ki dan duk dangin ku ba sa'a na. Wani wawan birki ta ja har tana kokarin faduwa ta ce"kaiiiiiiii! Amman kai mugun makaryaci ne, tsabar raini da rashin ta ido ni zaka kalla kace min duk dangin mu ba sa'an ka, toh ina ka aje aboki balle kuma yaya mugu ehhhhhh!, ko dai abinda ka ke sha ne ya fara dagula maka lissafi, kun san ku samarin zamanin nan ba a raba ku da aaaa, ta fada tana gwada mishi yanda ake shan taba". Iya kuluwa ya kulu ya dade yana jin irin rashin mutunci da takewa mutane, abin yau yazo kan shi, dutsen dake kusa da shi ya raruma zai Jefe ta da shi tsohon dake tsaye yana kallon su ya ce"kul dan nan kar ka kuskura", bata ko san suna yi ba dan tuni ta yi gaba............................ Mu haɗu da ku a cikin labarin..... Started Fri sep/12/2025 Finish................
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
18 parts Complete
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
You may also like
Slide 1 of 10
NANATOOU (DIYAR KAKA) cover
Solilovetude (Completed) [IDOL SERIES 1]  cover
MILIK MEGAT ZILL QAYYUM (TERBIT) cover
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅ cover
FATU A BIRNI (Complete) cover
I Got Love cover
AL'AJABIN SO cover
BAKAR WASIKA cover
SHAREEF 2023 cover
Penghulu Bidadariku S2 : Aisyah Humaira cover

NANATOOU (DIYAR KAKA)