Sunana Ummu Salma Ibrahim Mai Turare.Tun ina aji biyu na makarantar gaba da firamare Allah ya sanya mun son Uncle Bilal. Bansan ta ina zan fara yin bayani ba, amma bazan manta ba lokacin shekaru na goma sha uku, duk da kasancewar shi mutum mai shiru-shiru, baya son yawan magana amma yana da zafi idan aka yi mai laifi. Shine malamin da yake daukan mu darasin na'ura mai kwakwalwa. Lokaci daya muka neme shi a makarantar muka rasa, kuma har yanzu bamu sake ganin shi ba. Ni kuma ga soyayyar shi har yanzu ko da digo daya bata ragu ba. Ku taya ni nema a ina zan ga UNCLE BILAL?All Rights Reserved