YASMEENAH Da mamakance nake kallon kaina, ni ce amma bani bace! Bani bace wacce ke tsaye a gabana. Toh wacece ni ina kuma na tafi?, tambayoyi ne da ban da amsarsu don ko zaa shaƙe ni ba zan iya amsawa ba. A dai-dai lokacin bugun ƙofar shi ya tsananta " ki buɗe ƙofar nan nace!", a tsawace yayi maganar hakan ne ma ya sake hargitsa ƴaƴan hanjina. Don tabbas ina jin tsoron haɗuwata dashi amma kuma nafi tsoron halittar da take gabana da suna na.......... Deejasmaah.