Rayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da kayan more rayuwa a zamantakewar aure, nayi tunanin ina ma talakan da bashi da komai na aura indai zai bani kulawar da nake buk'ata a duk sanda na nemi hakan. Na samu ciwon damuwa tun ina da k'arancin shekaru ba tare dana farga ba, bani da abokin shawara na kasance marainiya mara uwa da uba. Na tabbatar mijina yana sona nima ina sonshi, shin meye ya jawo min hakan ni Ameenatou Laifina ne ko kuma laifin sane?. Auren mai kud'i shine riba a koda yaushe, na kwana a gida mai kyau, na tashi a waje mai kyau, naci abinda nake so, na hau motar da nake so, naa kuma fita duk k'asar da nake so ba tare da damuwar komai ba. Wannan shine kwanciyar hankali da walwala mai kawo farin ciki da annushuwa a zuciyar wanda yake cikin ta. Tabbas ni Fiddausi sai na kasance matar mai kudi ko ta wacce hanya.