Kowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi.
Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi ba, sarƙar ƙaddara ke ta janta daga wannan tarago zuwa wancan ko menene dalili?...
Labarin TUMUN DARE labari ne da ya faru a gaske, karanta don jin labarin yadda Hamra, marainiyar yarinya ta fuskanci ƙaddarorin rayuwa har ta kai ga ta cire buri ga farin ciki a duniyar, sai dai kwatsam ta samu soyayya daga mabanbantan wurare.