FITILAR KWAI

FITILAR KWAI

  • WpView
    LETTURE 1,429
  • WpVote
    Voti 32
  • WpPart
    Parti 37
WpMetadataReadIn corso6h 0m
WpMetadataNoticeUltima pubblicazione gio, giu 18, 2026
A wani zamani daya shuɗe, Da zarar magriba ta gabato kusan ko wani gida zaka riske su ɗauke da *FITILAR ƘWAI* Tun ba a fara min halitta ba na ke wahala, har tsahon watanni biyu a cikin ciki ina gwabzawa tare da mahaifata, ni ne ƙwan halittar dake cikin ta,ƙwan halittar da ake son a zubar. Kaifin kwakwalwar da Allah yayi ma jarirai ya sanya na ke fahimtar cikin labaran ta akwai rina a kaba. Mahaifiya ta ta shiga halin tsaka mai wuya, ta sha gwagwarmaya a rayuwar ta don kare ni daga magungunan da Abba na ya ke kawo mata don zubar da ciki na, Abba ya manta cewa mugun nufi, baya kashe ɗan barewa kuma da ikon Allah haƙan sa ba zai taɓa cimma ruwa ba akan gurbatacciyar buƙatar sa. A lokacin da sinadarin allurar ya feso zuwa mahaifar wato cikin in da na ke babu irin jijjigar da ban sha ba, maganin ya so ya tarwatsa sassan jiki na wanda bai da ɗe da zama tsoka ba, da ikon Allah na koma bayan mahaifarta na yi wa kai na ɓuya duk da tsananin wahalar da na sha tsakanin rayuwa ko mutuwa, Allah ya zaɓa min rayuwa, tsahon watanni shidda ina bayan mahaifarta sannan na dawo na zauna daram a cikin mahaifarta na kuma ɗaura daga kwanakin da na tsaya,lokacin na san da cewa kainuwa dashen Allah ne, haka zalika zakaran da Allah ya nufa da cara ana muzuru ana shaho sai yayi abin sa.
Tutti i diritti riservati
#76
hausalovestory
WpChevronRight
Entra a far parte della più grande comunità di narrativa al mondoFatti consigliare le migliori storie da leggere, salva le tue preferite nella tua Biblioteca, commenta e vota per essere ancora più parte della comunità.
Illustration

Potrebbe anche piacerti

  • MIJIN TSOHUWA
  • SAFEENATU
  • KOWA YA GA ZABUWA...
  • ZARITH'S: HER COMMANDO [C]
  • Asmaraloka Saptakāla [COMPLETED STORY]
  • Kupu-Kupu Jangan Pergi [18+ End]
  • KUSKURE
  • KAICO NAH
  • BAKAR WASIKA
  • AL'AJABIN SO

Duniya ba ta taɓa zama yadda mutum yake zato ba. Wasu na farin ciki ta hanyar da ba su taɓa zato ba, wasu kuwa sukan faɗa baƙin ciki ta hanyar da suka fi zaton samun farin ciki,Akwai lokaci da soyayya ke zama rahama, wani lokaci kuma kan zo saɓanin hakan. Hakan ce ta kasance cikin labarin Rayyan, saurayi kyakkyawa, mai hankali da buri, amma ƙaddara ta haɗa shi da tsohuwa, wacce duniya ta kira Hajja Hafsah - mace mai shekaru da dama, mai kuɗi, mai mulki, amma mai zurfin zuciya da ɓoyayyun sirai. Soyayya tsakanin saurayi da tsohuwa ba ta da sauƙi. Amma me zai faru idan abin da aka ɗauka wasa ya zama gaskiya, abin da aka ɗauka abin dariya ya zama abin kuka? Ku shigo, kuji mai zai faru.

Più dettagli
WpActionLinkLinee guida sui contenuti