"Kai ka sanya min sutura a lokacin da nake tamb'elen da soyayyarka ta jefani, kai ka jawoni inuwa a lokacin da zafin rana ya isheni nake neman inda zan saka raina naji sanyi, kaine wanda ya share mun hawaye a lokacin da suke gudu a kuncina na rasa wanda zai shareminsu, kaine ka jawoni a jiki a lokacin da kowa ya tureni, kaine soyayyarka ta rufe mun ido na kasa gane zab'in da iyayena suka min, kaine wanda naso tun duniya tana bacci baka tara abun cikinta ba, haka kuma kaine wanda na runtse idona nayi fatali da zab'in Abbana, ta dalilinka ne na shafawa idanuna toka nayi fatali da kunyar da ubangiji yayi min a matsayina na 'ya Mace halitta mai tsananin kunya, nace musu ga wanda nake so, haka zalika kaine wanda na shiga wahalar rayuwa ta dalilin aurenka, kaine Wanda nake danne yunwar cikina saboda kai a lokacin dana kalli abincin daya rage iya cikin mutum daya zaiyiwa nakan hak'ura da nawa yunwar na bar maka... Akanka ne na fara sanin danne damuwa, duk wata wahala ta rayuwar duniya ta dalilinka ne ta sameni, nayi kuka a boye akanka nayi a bayyane, amma ban taba barin kaga hawaye na ba saboda gudun tashin hankalinka, hatta suturata sai dana siyar saboda neman yadda zamu rufawa juna asiri dani da kai, daga k'arshe a ka yayemun suturan daka sanya min a kasuwa a gaban bainan nasi, haka kuma ka turani ranar da ka jawo ni ba tare da tunanin zafin ta ba, Abdul-razak ka wulakantani! ka tozartani! kayi min abunda babu wanda zai min irinsa, kai butulu ne, ka kasance mai saka alkhairi da sharri, nayi maka dare kai kuma kayi min rana, tabbas namiji ba d'an goyo bane a yau na tabbatar, haka kuma na gane duk d'an daya hana uwarsa bacci, to shima bazai rintsa ba tabbas na fifita sonka akan biyayyan iyayena nayi kuskure mai wuyar gyaruwa. Ta ida maganar idanunta suna zubar da hawaye na zallan bakin ciki da kaico....
Lian snuck out of the imperial palace and exposed the village healer to be a fraud and a devil-worshipper. Cursed by the spurned fire god, Huogwai, and disgraced and cast out by the royal family, Lian set out with her manservant Emiru to the kingdom of fire to rid her of the curse of uncontrollable flames for a chance to regain her claim to the throne. But being a fire disciple meant she was a practitioner of the forbidden arts. For those that hunt her kind, the game had just started.