Maɓudi بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ A YAYIN DA WASU KE WALWALA, A LOKACIN NE MU KUMA MU KE BIN LUNGU DA SAKO, KWARARO-KWARARO DOMIN NEMAN ABIN SAKAWA A BAKIN SALATI. WASU SU BAMU DOMIN ALLAH CIKE DA TAUSAYAWA, WASU KUMA SU BAMU SUNA MITA, HANTARA, KYARA TARE DA TSANGWAMA, KAI HAR DA MASU ALLAH WADAI DAMU MA. KALMOMIN "ALLAZI WAHIDI, A TAIMAKA!". Su ne kalaman da ke tashi a cikkn dandazon al'ummar da ke cuɗanya tare da kaiwa da komowa wajen hada-hadar kasuwanci. Dubannin mutane da cikin kasuwar Ceceniya da ke kan titin Ahmadu Bello a cikin garin Kaduna. Kalmar "Wahidi" ita ce ke fita daga bakunan yaran da ke riƙe da robobinsu na bara, waɗanda suka kasance ƙanana mabambanta da shekarunsu ke tsakankanin bakwai zuwa goma sha biyar. Ta ɗaya ɓangaren kuma sahun manya ne da za mu iya cewa iyayensu ne haɗe da tsofaffi, wasu daga ciki masu naƙasa wato guragu, makafi, kutare da dai sauransu. Ta ɗaya ɓangaren kuma daga inda almajiran suke, wasu ne zaune cikin shigar manyan suturu tare da Rawani, alamun da ke nuni da yanayin sarauta kenan daga cikinsu ko ba a sheda maka hakan ba.