Tashi yayi a sanyaye ya fita ya daga falon dan zama a ciki zai iya saka shi hauka na wucin gadi, mota ya shiga ya fita daga gidan a guje. Sai da yayi nisa ya tsaya a kan hanya ya kifa kansa a kan sitiyarin motar cikin tashin hankali da tsoro mai yawa. Zuciyar sa bugawa take yi sosai ji yake kamar yayi hauka, tunanin sa yana ga abinda Abba ya faɗa masa, da gaske dai matar Manal ƙanwar sa ce ta jini ko wasa ake masa?, in hakan ya tabbata ya zai yi? In hakan ya tabbata me zai faru wanne hali zai shiga? In hakan ya faru ya zai yi da ransa?. Allah ya sani yana matuƙar qaunar Manal, yana kallon ta matsayin abokiyar rayuwar sa kuma bugun zuciyar sa, kallon matar sa ma'ajin sirrin sa yake mata, kallon Manal yake matsayin uwar yaron sa da yake cikin ta. Taya rana tsaka ake so a juya ta ta koma ƙanwar sa wacce suke uba ɗaya?, in hakan ya faru da wanne ido zai iya kallon ta matsayin ƙanwar sa da suke jini ɗaya? Ya matsayin ɗansa da yake cikin ta? Ɗan sa ne ko ɗan ƙanwar sa?.All Rights Reserved
1 part