Story cover for 💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream ) by faizamurai
💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )
  • WpView
    Reads 8,338
  • WpVote
    Votes 160
  • WpPart
    Parts 25
  • WpHistory
    Time 13h 23m
  • WpView
    Reads 8,338
  • WpVote
    Votes 160
  • WpPart
    Parts 25
  • WpHistory
    Time 13h 23m
Complete, First published Mar 31, 2024
Haka take ta faman Lilo da k'afafun ta tare da sakin k'ayataccen murmushinta,tana cigaba da binsa da kyawawan idanunta masu haske kamar wata k'aramar yarinya cikin Rashin damuwa tana k'ara fad'ad'a murmushin ta Wanda ke nuna Babu abun da ke damunta ayanzu.

A hankali Kuma murmushin Dake ke kwance akan kyakkyawar fuskar ta yafara gushewa inda ya koma b'ata fuska sai Kuma kuka , inda ta bare d'an karamin Bakin nata kamar wata k'aramar yarinya tana kuka,haka take sakin kukan Mai had'e da shagwab'a.Dr Ammar Dake kallon ta cikin tausayin ta da Mamakin lamarin nata ganin murmushin ya gushe lokaci d'aya sai Kuma kukan da ta fara Wanda duk da yake ba Mai sauti ba ne,Amma haka yake Jin sa har tsakiyar kan sa inda Kuma take zuciyarsa ta fara bugawa yadda take kukan kamar tana tafiya da zuciyarsa ne yadda kukan ke ratsa shi,Bai ce mata k'ala ba ko ya rarrashe ta sai ma Lumshe idanun sa da yayi Jin yadda suka Kara yimasa nauyi. Itama bata Wani damu ba Wanda ita kanta bata San ko kukan mene ne takeyi ba in aka tambaye ta.Ganin ya zuba mata manyan idanun nasa har baya son k'yaftawa kamar an mintseleta ko ta tashi da sauri tana sauko da k'afafun ta daga kan gadon tare da share hawayen ta da suka kasa tsayawa tana tsayar da kukan cak. Dai daituwar tsayin nata Gaban sane ya bata damar rik'e k'ugun ta cikin
All Rights Reserved
Sign up to add 💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream ) to your library and receive updates
or
#17kaddara
Content Guidelines
You may also like
 AFRA  by Smiling_Bay
57 parts Complete
Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta buga akan speakern dan ta ga ko yana aiki. Illai kuwa sai ta ji ƙaran bugun da tayi. Murmushi ta ƙara sakar wa mutanen da duk ita suke kallo, da mamaki a idanuwansu, kafin ta buɗe baki tafara magana kamar haka. " Assalamu alaikum " sai ta ɗan dakata kaɗan don su amsa mata, ba laifi wasu sun amsa mata wasu kuma sunyi ƙum da bakin su. " dama na zo ne don na nuna farinciki na game da taya abokin mu, kaninmu da yayen mu Salim murna " tace yayin da take kallon angon wanda tun tahowarta stage yake warwara ido kamar baƙin munafuki, gashi yanda zufa yake ta keto masa, zaka zata ba ac a wajen. Kau da idanunshi yayi kafin su hadu da nata. " amma kuma abin da ya sosa min rai game da wannan abin shine ni nafi chanchanta da a kira in zo in bada tarihin wanan bawan Allah. " ta ƙara dan dakatawa yayin da ta runsunar da kanta kamar mai wani tunani, sai kuma ta k'ara daga kanta ta kalle mutanen da duk suke yi mata kallon mahaukaciya wadda batasan abin da take ba. Budar bakin ta ne sai tace. " duk da dai an kira abokin ango yayi nasa bayanin barin in ɗan baku tak'aitaccen nawa ". " amarya Salima " tace tana kallon amaryar da tace kwalliya a cikin doguwar riga kalar ja itama, sai dai na amaryar bai kai na wannan budurwar kyau da tsaruwa ba, dan inbaka san wacce amaryar ba sai kazata itace. Salima wacce tun da yarinyar tafara magana ta ke ta faman bankamata harara, taja wani ɗan tsaki game da sake sakarmata wani hararan. Afra , yarinyar da ta ke kan stage in ta murmusa kafin tace ." ina taya ki murnar auran munafukin namiji, azzalume wanda bai san darajar mutane ba, ina kuma ƙara tayaki murnar samun daƙiƙin na namiji wanda ban da wata shakka ƙarshen sa bazai yi kyau ba, kuma ki kasa kunan ki kiji mijinko mayaudari ne, me bin mata ne kuma zan iya rantse miki fasiƙi ne " Read and find out
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
18 parts Complete
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
You may also like
Slide 1 of 10
Sex and Death in Skeleton City cover
MATAR AMEER cover
MAI ƊAKI...! cover
  SARK'AK'IYAR SOYAYYA! cover
TAFIYAR MU (Completed) cover
SOYAYYA KO SHA'AWA cover
KALLON KITSE cover
 AFRA  cover
FATU A BIRNI (Complete) cover
RUWAN DAFA KAI 1 cover

Sex and Death in Skeleton City

29 parts Complete

Geoff and Naomi are dead, and they're depressed, but when Geoff's cat Bernie dies as well, they embark on a wild journey to find it in the underworld. ***** When Geoff dies, alongside his girlfriend Naomi, they end up sharing an apartment in the Underworld as skeletons. But after a few years, Geoff starts suffering a mid-death crisis. What's the purpose of going through the motions as a skeleton if you can't really live? Then he gets word that his cat, Bernie, just died and he can collect him and bring him home! Geoff and Naomi hurry to get Bernie only to discover that, due to a clerical error, their cat has been lost. With the hunt for Bernie giving new purpose to Geoff's un-life, he and Naomi begin a quest to get back their cat. Battling skeleton pirates, climbing the sky ladder and facing off against the villain who took Bernie, Geoff is determined to find his purpose - or die a second time trying! [[2018 Wattys Winner - The Originals]] [[word count: 30,000-40,000 words]]