ILHAM
  • Reads 23,668
  • Votes 2,333
  • Parts 48
  • Time 10h 12m
  • Reads 23,668
  • Votes 2,333
  • Parts 48
  • Time 10h 12m
Ongoing, First published Apr 04, 2024
2 new parts
A rayuwar Ilham Bukar bata qaunar a wulaqanta ta don haka Idan har kana so ka zauna lafiya da ita toh kar ka wulaqanta ta.....!
All Rights Reserved
Sign up to add ILHAM to your library and receive updates
or
#169life
Content Guidelines
You may also like
AURE UKU(completed) by Chuchujay
32 parts Complete
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace mara san hayaniya wadda tasan kan Aikinta ,babu abunda tasa a gabanta illa bawa Aikinta babban muhimmanci kana yaranta wadda kaɗdarar samunsu ta rarraba mata Aure . Kalma ɗaya zaka faɗa ta bata mata rai shine kushe mata Aikinta ko nuna wasa a duk wani abu da ya shafi Aikinta . Ita ɗin kwarariyace kuma gogaggiya akan duk wani abu da ya safi surgery,ba kasar ta ba hatta a wasu kasashen tana zuwa aiki. Bangaren soyayya fa? Bata dauki soyayya a bakin komai ba tunda dukkan Aurenta guda ɗaya ne tayi na soyayya kuma shima bai karbe ta ba wanda hakan yasa ta yanke shawarar saka soyayya a ƙwandan shara duk da kuwa tayin da ake kawo mata ,ta gama yanke imani da soyayya akan duk wani ɗa namiji wanda haka yasa mutane da dama ke mata kazafi da mata take so duba da ƙin mazanta karara a fili. Amma menene dalilin tsanar tasu da tayi? Menene yasa ta cire mazan daga tunaninta da zuciyarta baki daya? Shin zata faɗa soyayyar wani ɗa namiji ko a'a? Idan zata faɗa wanenen wannan mai sa'ar?. DR IMAM MUKTAR PAKI, Saurayi dan kimanin shekaru Ishirin da tara ,bai taba Aure ba, Dalibi wanda yake neman sake gogewa akan Aikin surgery ,shekara ɗaya wadda kareta ne kaɗai zai bashi kwali da kuma lasisin Fara yin surgery ,kaddara itace tayi aikinta ta ɗauko sa kan kachakar ta kawosa CITY TEACHING HOSPITAL inda yake ƙarkashin jagorancin likitar da kowa ke tsoro da shakka, Mene zai faru idan shi bai ji wannan feelings ɗin ba sai wani daban wanda shi kansa bazaya iya fassarawa ba? Shin ya wannan kaɗdarar tasu zata kasance? Shin Wanne irin chakwakiya Imam ke shirin ɗaukowa kansa domin wannan likitar da ya ke kan giyar so AURENTA UKU ,Ƴaƴanta uku a yayin da shi ko na fari bai taba yi ba. Ku biyo ɗiya jamilu domin jin yarda wannan labarin na IMAM da UMAIMAH zai kasance !
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
18 parts Complete
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
You may also like
Slide 1 of 10
MAI ƊAKI...! cover
Ramin karya (Hausa novel )completed cover
Khadeejarh ❤️❤️ cover
KALLON KITSE cover
AURE UKU(completed) cover
OUR DESTINY  cover
BIYAYYAH cover
MATAR KULLE(Short story) cover
MENENE MATSAYINA... cover
FATU A BIRNI (Complete) cover

MAI ƊAKI...!

22 parts Complete

Rayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da kayan more rayuwa a zamantakewar aure, nayi tunanin ina ma talakan da bashi da komai na aura indai zai bani kulawar da nake buk'ata a duk sanda na nemi hakan. Na samu ciwon damuwa tun ina da k'arancin shekaru ba tare dana farga ba, bani da abokin shawara na kasance marainiya mara uwa da uba. Na tabbatar mijina yana sona nima ina sonshi, shin meye ya jawo min hakan ni Ameenatou Laifina ne ko kuma laifin sane?. Auren mai kud'i shine riba a koda yaushe, na kwana a gida mai kyau, na tashi a waje mai kyau, naci abinda nake so, na hau motar da nake so, naa kuma fita duk k'asar da nake so ba tare da damuwar komai ba. Wannan shine kwanciyar hankali da walwala mai kawo farin ciki da annushuwa a zuciyar wanda yake cikin ta. Tabbas ni Fiddausi sai na kasance matar mai kudi ko ta wacce hanya.