8 parts Complete 'Ta dan juya kanta cike da mamaki, tace, "Daddynka kuma? wanene shi?"
Yace, "Habib Abdullahi Makama?!" cikin sigar tambaya.
Jin sunanshi kadai ma sai daya sanya taji bugun zuciyarta ya canza. A duka kwanakin da suka wuce tun bayan daya ajiyeta a kofar gidansu ya wuce, karya take yi tace babu wata rana da zata fito ta koma ga mahaliccinta bata tunano wannan mutumin ba. Abin har ya kusa zame mata jiki, yin tunaninshi a lokacin da taje yin kwanciya barci. Wasu dararen kuwa har da mafarkinshi da tunanin wannan daddadan kamshi nashi, wanda ta lalubo turaren da yake amfani dashi cikin wadanda ya bata, itama ta mayar dashi nata turaren. Yaudarar kanta take, da take cewa wai tuni ta manta da sha'aninshi da kurar data kwasoshi. Ita tasan karya take yiwa kanta.
Duk kuma yadda taso abinda ke tukarta a zuciya kada ya bayyana, sai daya bayyana din. Ta rasa fara'ar kirkirowa tayi koda ta yake ce kuwa, haka bugun zuciyarta ya ki saisaituwa duk yadda taso ta saisaita shi kuwa.
Ta daure dai da kyar tace, "ok, na ganeshi. Yana ina yanzu?"
Ya dan daga kafada, "ban sani ba nima. Kawai dai yace in zauna a wajenki zai dawo ya daukeni."
Ita abin ma sai ya girmame mata, mamaki ya hanata motsi. To ita kuma a su wa? Kuma da wane dalili? Da zai dauko danshi ya kai mata?..."
To domin sanin dalilin, don me, kuma me yasa? Sai ku biyoni Ni Jeeddah Lawals tare da Nadiya a wannan tafiyar tamu.