So da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda na kasa fin karfin zuciya ta in karba nasa kafa nayi shuri da ita. Abinda na manta shine a lokacin da wani ya jefar da abinda yake ganin ba shi da amfani gare shi, a lokacin ne kuma wani zai tsinta ya danke da hannu bibbiyu. Ya so ni da dukkan zuciyar sa, ya kauna ce ni da gaba daya rayuwar sa haka kuma ya bauta min da duk lafiyar sa, amma da me na saka masa?, da mafi munin sakayyar da duk wani dan Adam ze jura. Na wulakanta shi a inda ake ganin darajar sa, na zubar mai da kima a inda ake mutunta shi, kai nayi masa abubuwa da yawan da duk ya jure har zuwa lokacin da ƙaddara ta raba mu ta karfi da yaji wanda na bada gudunmawa ga wannan ƙaddara ba kadan ba. Sedai ba'a dauki lokaci me tsayi ba na gane nice da asara, haka kuma abinda na kwallafa rai din ban samu ba, banda gare gare da kwallon da ƙaddara ta dinga yi da rayuwa ta. A lokacin da ya hakura dani taa dole, ya karbi ƙaddarar rayuwa da zavin Ubangiji gare shi, a lokacin ne wata kaddarar ta sake daure zare me karfi tsakanin mu. Shin da wani ido zan dube shi, da wane karfin halin zan yaki rauni na na karbi kyakkyawar ƙaddara ta?, shin shi ɗin ze bani dama ko kuwa ya rufe babi na? shin har yanzu akwai digon alfarma tsakani na dashi???? #Aimah #Sa'adah #Masdooq #hatred #jealous #depression #destiny all in; #love_story_2024
56 parts