Ban taɓa zuwa asibiti ba tunda nake a rayuwata ba, mu 'yan gargajiya ne, sai dai karon farko dana je asibiti shi ne abu na biyu daya ƙara ruguza rayuwata. Na shiga ɗimuwa, na yi nadamar da ban taɓa yin irinta a rayuwata ba, wani lokacin idan na kalli kaina sai naga kamar ni kaɗaice Allah ya jarabta da mummunar ƙaddara irin wannan, sai dai wasu lokutan sai na tuna cewa wannan ba komai bace face jarabawar rayuwa. Ni aure sam bai min rana ba, har mamaki nake idan wasu na farin ciki da aure, ni aure a damuwa ya jefani wadda tayi min tabo na har abada! Ku biyoni cikin labarin dan na warware muku zare da abawa.All Rights Reserved