********** SALEEM*******
Ashekaruna na ashirin da takwas ,ina nufashine saboda Abu daya.Daukan fansar mutuwar mahaifina,wacce Wadda Zai aura ta hallakashi har lahira.
Sunana SALEEM ABDULLAHI SILFU ,Daga margayin Sarkin TUNBUTU ,kuma Yarima Mai jiron Gado.Mahaifiyata tarasu wata bakwai da rasuwar mahaifina,ina Shekara bakwai lokacin damuka riski wannan bakin labarin,kuma alokacin ne nida mahaifiyata da Yan uwana muka yi mugun ganin gawar mahaifinmu,munshiga bakin ciki har ciwo yakwantar da mahaifiyata Indata muka rasata,,,,
Nagirmane agurin yar uwar mahaifiyata Gimbiya Sakinat Songhai,ina kiranta da Ammi,,,
Labarina yafarane tun Kafin a haifeni,mahaifina shine kanin Sarkin kasar TUNBUTU,kasancewarsa sadauki da kuma dabia tagari yasa mahaifinsu yanemi da KO bayan ransa aba dansa na biyu mulki ,hakane kuma yafaru aka nada mahaifina maimakon yayansa Wanda Suke uwa daya uba daya,kawuna Sarkin TUNBUTU nayanxu yakasance ubane ga yaya Mata guda goma Inda yarasa yayansa Maza guda uku a yaki,ayanxu yakeda Shekara tamanin a duniya,ya auri Mata Sama da bakwai domin samin magaji Amma Allah be nufeshi da haihuwar namijiba tun bayan yayansa guda uku da yarasa a yaki,,,,,,,
Nakasance nine da na fari agurin mahaifana,inada kanne Maza biyu da kanne Mata guda goma sha uku,,Yan uwana Mata kowaccensu Tayi aure a karamin nahiyoyin dake kasar Mali kuma suna zaune cikin kwanciyar hankali,kannena Maza kuma suna London karatu,,,
Ayanxu dole nine sarki Mai jiran gado a garin TUNBUTU,Amma sarki yafi kaunar dansa nacikinsa yagajeshi,,,, wannan shine kadan daga cikin rayuwata ,,kaddara tasa narasa iyayena a kananin shekaru Inda ayanxu nake rayuwa kamar wani bawa,kanne na bakamar yayan sarauta domin kawuna Baya kuladamu kuma Baya kaunarmu saboda laifin mahaifinmu dayake gani Wanda har soyayyar yake wa mace yakaita GA bashi poison yasha ya mutu,Saboda kawai bashi take kaunaba ,Dan Sarkin kasar Bamak
All Rights Reserved