Story cover for CIWON ƳA MACE.. by Ouummey
CIWON ƳA MACE..
  • WpView
    Reads 2,938
  • WpVote
    Votes 111
  • WpPart
    Parts 16
  • WpHistory
    Time 3h 4m
  • WpView
    Reads 2,938
  • WpVote
    Votes 111
  • WpPart
    Parts 16
  • WpHistory
    Time 3h 4m
Ongoing, First published May 19, 2024
Rayuwa cike take da kaddarori da dama, dan Adam baze ce tayi imani ba kuma Allah ya kyale shi kawai, dan yadda da wannan imanin se Allah ya rubuto series of jarrabawowi din tabbatar da ingancin imanin namu.

Se dai san rai da son zuciya na jagorantar dan Adam ga munanan ayyuka, wanda daga karshe suke jinginawa ƙaddara, akwai ƙaddara, amma kuma a boye cikin kaddarar nan akwai jagorancin wasu munanan halaye, son kai, hassada, bakin ciki, da ire iren su.

Akwai wani karin magana da Bahaushe ke amafani da shi,musamman a tsakanin mu mata, wanda nake da ja akan shi, da kwarin gwiwa ta, da dukkan zuciya ta, haka da dukkan murya ta nake faɗin CIWON ƳA MACE BE TAƁA ZAMA NA ƳA MACE BA!.

Ban yarda da karin maganar wai CIWON ƳA MACE NA ƳA MACE bane, ban kuma aminta ba, shiyasa tun tasowa ta nayi watsi da shi, bangarori da dama da na duba na rayuwar mu mata ya karya ta shi.

Ina tunanin bahaushe be fahimci rayuwar mu ba, be karanci mata ba, da na tabbata baze fadi wannan zancen ba balle har ya shiga jadawalin karin maganar mu na Hausa masu tushe da dimbin tarihi.

Bari kuji, mace ita ce matsalar mace yar uwar ta, dukkan kukan mace in kun yi duba daga tushe zaku ga daga mace yake, kyashi, bakin ciki, hassada, son kai,  munafunci da wasu sauran mugayen halaye da dabi'u sun tare a wajen mata ne.

Ba zan ce duka ba dan ko a cikin gidan karuwai akan haifi malami, sedai da yawan mu haka muke, bana tunanin akwai macen da in aka binciki rayuwar ta ba za'a samu tabon yar uwar ta mace ba, in one way or the other, se kuma da na fara fahimtar rayuwa na fahimci DOLE ACE MATA SUN FI YAWA A WUTA.!

Ban tsani mace ba dan nima itace, mahaifiya ta ma itace, akwai kuma tarin yayye da kanne, sedai na tsani munanan halayen mu, na kyamaci gurbatattun mata na daga cikin mu, dan sun taka rawar gani cikin KADDARAR RAYUWA TA!.

Dan Allah kar ku yanke min hukunci batare da kun saurare ni ba, ina rokon ku ku bani aron lokaci da hankalin ku, ku biyo ni dan jin muguwar rawar da mace ta taka cikin ra
All Rights Reserved
Sign up to add CIWON ƳA MACE.. to your library and receive updates
or
#21kaddara
Content Guidelines
You may also like
RUHI BIYI (a gangar jiki daya) by Abdul10k
24 parts Complete
Hakan ya furta cikin kasar zuci,amma ko cikin karfi irin ta tsatsuba Nainah ta saurari komi....... Gajeriyar murmushi tayi,daga karshe ta hade fuska......nanfa ta soma tunano abinda ya faru a wancen lokacin.....da kuma abinda yayi sanadin sumewar Harun. A yayin da Harun ke Yunkurin taba kafadar wannan halittar data diro masa a gaba..... sai bakaken aljanun nan suka sake bayyana inda suka aika sakon tsafi....wacce tayi sama da Harun din ta kuma bugasa da kasa..... Cikin kankanin lokaci ya sume....Nainah da ganin haka ta hade rai hade da cewa.... "Kai kananun masharranta mai kuke takama dashi da har zaku sumar da wanda nake karewa...."?? *Karku shige rudani _readers_ dan wannan wanda ta diro gaban harun ba kowa bace illa Nainah....* Dajiyo batun nata ko daya daga cikin bakaken aljanun ya koma bayan babban nasu yace dashi...... "Yaya Gafur.....ninasan hatsarin wannan Yarinyan.... Itace fa wannan gimbiya danake baka labarin wato Nainah.........ita tayi sanadiyar mutuwar Gwarzon mayakan Bakaken aljanun na saman tsauni...." Dajiyo hakan ko Gafur ya fashe da muguwar dariya hade kuma da kyakyatawa....cikin murya uku uku Sannan yace da dan uwan nasa........ "ba gimbiya take ba...ko itace sarauniyar aljanun duniya,tunda dai ta shigo gonata saina koya mata hankali" Haka kannen nasa sukayi ta kokarin tsayar dashi amma yaki sauraron su... Dukda ma kannen nasa akayima abin amma hakan ta matukar hassala shi... Nainah ko....motsawa batayi ba,ta wani bushe kim guri guda... Nanfa gafur ya umurci kannen nasa da su basa guri.... Sannan yaja layi ya soma aika sakon tsafi iri iri...
KUSKURE by Shatuuu095
15 parts Ongoing
Hannu na karkarwa yake, jiki na har bari yake, saboda tun da nake Rai na Bai taba baci ba kamar yau, ban taba tunanin Baba zai iya abin da yayi yau ba, na saka hannu na na toshe kunne na saboda na daina Jin muryar shi, Amma tamkar a gaba na yake ihun, tamkar ni din yake yiwa masifa "...Saboda ke Baki da mutunci, ke ba yar mutunci bace ba, har ni zance kiyi Abu ki kiyi, to se de ki bar min gida na yau dinnan, ki fito ki hada kayan ki ki bar min gida na, ni ba shashan namiji bane ba..." He kept on saying, ya cigaba da fada Yana yarfa zagi, na zata zagi na Yan kauye ne, na zata ana yin zagi ne ga mutanen da ba su da ilimi, se gashi Baba ne yake zagin Mama a tsakar gida, a gaban mu, gaban kishiyar ta, gaban almajirai, masu aiki yake mata wannan cin mutuncin, nasan ya taba, ba sau daya ba, ba sau biyu ba Amma Bai taba cin mata mutunci irin na yau ba, a gani na ko Babu komai ya kamata taci albarkacin mu, ya kamata ya daga mata kafa saboda mu, se naji zuciya ta tana zafi, tana zugi na kasa hakuri na fito daga dakin, Kai a lokacin ma it's as though I'm possessed saboda wallahi kwakwalwa ta bata tare da ni, zuciya ta ce kawai ke fada min kada na bari, kada nayi shiru cin mutuncin yayi yawa, na kuwa fito tsakar gidan, gidan yayi tsit saboda Baba ya gama ya wuce dakin shi, se almajiran mu biyu suna yiwa Amarya shanyar labule da suka wanke mata, na wuce su na nufi dakin shi fuska ta tayi Wani irin ja, hatta wata vein da nake da ita a goshi na ta fito, tabbacin Rai na ya baci, Yana zaune na same shi a parlon shi, na kalle shi saboda ko sallama banyi ba shi ma ya kalle ni nace "Baba! Me yasa zaka dinga cin zarafin Maman mu a gaban mu, a gaban kowa a gidannan, me tayi maka?" Se ya dago ya kalle ni, I can see the amazement in his eyes, saboda yayi mamaki, baiyi tunanin bakar zuciya ta har ta Kai haka ba... Inaaya
🌸RAYUWAR MU A YAU🌸 by faizamurai
40 parts Complete Mature
Bai furta mata komai ba kawai ya ɗago wuyan ta da wani irin ƙarfi ya kafa mata a baki bata Musa ba kuwa ta haɗiye ta duk wadda ya juye mata a baki saboda tana da ɗan yawa har tana ɗan zuba a gefen bakin ta. Wadda ta zuba a gefen bakin na ta ya fara lashe wa kamar wani maye kafin a hankali ya zare rigar jikin ta ya fara tuttula mata madarar. A hankali yake bin jikin na ta da ya tsiyaya madarar yana lashewa tare da wadda ke ƙoƙarin sauka a jikin ta kamar wani tsohon maye.Nadiya kuwa an samu abun da ake so sai ƙara gantsarewa take yi tana sakin ƙananan nishi bai daina ba sai da ya suɗe ta tass sannan ya koma kan lips ɗin ta suma Nadiya kuwa take ta fara mayar masa dan haka kawai ta samu kanta da kasa mayar masa kamar yadda suka saba tun kafin Auren su da kuma kasa aiwatar da komai kamar yadda ta sanar wa da ƙawayen su da shawarar da suka bata da ɗaura ta akan mugun saiti.Wani irin zut zut take ji a jikin ta wanda lokaci ɗaya wata irin buƙata ta taso mata maganin da ya saka mata a madarar ya fara ta siri.Jin sabon salon da ya ɗauka hakan ya sa ta kasa haƙuri ta fara sakin wani irin Shegen kuka mai tayar da tarzoma.Ai ko kamar ta ƙara ma Tanim ƙaimi.Jin jikin ta ya fara saki hakan ya sa babu Addu,a babu komai ya afka mata kamar wani Akuya haka yake mu,amalantar ta Nadiya kuwa ta kasa kuka duk da azabar dake ratsa ta sai dai maganin yana son ya rinjaye ta Dan ma tana da karfin Jini ne. A wannan dare ne Tanim ya cika burin sa ya kore ƙishin sa akan Nadiya,ƙishin da ya daɗe yana Dannewa ƙishin da ya lulluɓe da sunan soyayya,ya tsinci kanshi cikin farin ciki domin kusan zaucewa yayi zagayen da yayi akan ta kuwa ya kusan bakwai kasancewar ya sha maganin da yafi ƙarfin jinin sa shima.Dukkanin su sun jigata sai dai hakan bai hana komai ba saboda
SAWUN GIWA...!🐘 by Hafnancy01
18 parts Complete
"Dallah gafara can malama, har ke kin isa ki mana abunda Allah bai mana shi ba? Akanki ne aka Fara irin hakan? Ko kuwa akanki ne za'a daina? Sai wani ciccika bak'in banza kike awurin kamar zaki iya tabuka abun kirki idan har mukayo gaba da gabanta, Ke kin sani sarai ba yabon kai ba ammh wallahi tsab zan tumurmusheki anan wurin kuma in zauna lfy lau agidan Mijina, Kuma ki saurareni dak'yau, halinki ne ya jaza miki wannan cin amanar, Ke kowacce mace tana mafarkin samun miji kamar naki ammh ke Allah ya baki salihin mutum mai tsoron Allah, Sai ke kuma kikai amfani da hakan kina muzguna masa? Bashi da iko da gidansa sai yadda kikai? Babu wata muryar da yake tsoro da shakka face naki? To wallahi ki sani da'ace ayau bani da aure ne to Kinji nace Allah mijinki zan aura, zan shawo kansa kuma dole ya saurareni don kowacce mace da salon nata kissar, balle ma idan yaga ina masa abunda ke baki masa shi, kin san Zuciya nason mai faranta mata, ke mahaukaci kankat kenan yana kaunar mai faranta masa balle mai hankali, Hajiya Sa'a kiyi kuka da kanki ba dani ba don iya allonki ne yaja miki Faruwar hakan." Kuka sosai Hajiya Sa'a ke rerawa don ta kasa Furta komai kuma, Hajiya Aisha ta gama kashe mata jiki, Kama baki Hajiya Aishar tayi tana Fadin"Ai baki ma soma kukan ba, nan gaba kadan zakiyi wanda yafi wannan, kuma ki saurareni dak'yau, ga 'yata nan amana, Ku Zauna lfy ke da ita don wallahi kika sake naji ance ko ciwon kai kin sakata Allah saina lahira ya fiki jindadi, don kwarai zan cire kunyar Surukuta da amintar dake tsakaninmu musa wando kafa daya dani dake, Sabida haka ki kiyaye sannan Kuma akyalesu su sha amarcinsu Cikin kwanciyar hankali, don wallahi Hajiya Sa'a tashin hankalinsu kema tashin hankalinki, Tun wuri ki iya takunki don karki ce ban fada miki ba, Suhaila ita kadai ce 'yar da Allah ya bani sabida haka zan iya yin komai akanta, Ki huta lfy."
NANA AMINATU 2022 by UmmuDahirah
56 parts Complete Mature
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.
GADAR ZARE by HauwaAUsmanjiddarh
80 parts Complete Mature
A firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu yana yarfa hannunsa, zumbur ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko robar ruwa ya bulbulawa kansa "Akan ido na suka k'one gidan mu, mahaifiya ta, mahaifi na, k'anne na duk suka mutu akan kunne na ina jiyo ihun su *************** "Cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa bansan wanda yayi min ciki nan ba. Kanta tayo gadan-gadan tana nizaki rainawa hankali, ta shak'e ta idonta suka kakkafe ************** A cikin gidan yarin yake ihu yana kuka yace " sunci Amana ta, sunyi min butulci, na yarda dasu amma sun ci min amana sun had'a min GADAR ZARE Amintattu nane suka yi silar zuwa na gidan yarin, sun raba ni da kowa nawa sun raba ni farin cikina,cikin matsanancin kuka yace " wallahi koda zan rasa komai na rayuwata bazan kyale su ba. Sun mun sharri, sun had'a man makirci da GADAR ZARE ************* "Koken a cikin kayana kuma, kafin ya k'ara sa maganar dubbun police sun kewaye shi da bindugogi, Ana cikin haka wayarsa ta fara ringing, dakyar ya samu ikon d'agawa, ji yayi muryarsa ta tintsere da dariya yace " nine, d'an uwanka, kaga yadda nayi wasa da hankalinka ko, na nuna maka halin 'yan Adam Cikin rawar murya yace " mai yasa kaci amanata? " saboda ina santa, ita rayuwa tace kuma mallakina , Wani irin mahaucin ihu ya saki tare da buga wayar da k'asa .
You may also like
Slide 1 of 10
BAHAGON TUNANI  cover
KAICO NAH cover
RUHI BIYI (a gangar jiki daya) cover
KWANTAN ƁAUNA cover
KUSKURE cover
🌸RAYUWAR MU A YAU🌸 cover
SAWUN GIWA...!🐘 cover
NANA AMINATU 2022 cover
GADAR ZARE cover
💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream ) cover

BAHAGON TUNANI

16 parts Ongoing

_Ta ya kishiyar da ta shuka sharri ta yi tunanin girbar alkhairi_ _Ta ya kishiyar da ta tarwatsa farincikin abokiyar zamanta ta yi tunanin kwanciyar hankali zai aureta_ _HAFIZA natsattsiyar yarinya, mahaddaciyar Al'qur'ani da ta taso cikin kaɗaicin yayyenta uku da suke hannun kishiyar mahaifiyarsu,tana gana musu azaba sakamakon hatsabibiyar mallakar da ta yi ma Ubansu. Wani gigitaccen al'amari ya tilasta HAFIZA komawa wurin kishiyar mahaifiyarta sakamakon bangon da take kallo a matsayin majigini ya rushe. Kishiyar mahaifiyarta ta ci gaba ta soya musu tsakuwa a hannu yayin da ta keɓe yaranta tana shayar da su ruwan zuma. Sau biyu kishiyar mahaifiyarta na zama silar fasawan auranta ganin za ta fi yaranta jin daɗin gidan miji. Sai dai Ubangiji ya yi ikonsa,domin ta yi dacen miji ɗaya tamkar dubu wanda ya doke na sauran mazajen 'yan'uwanta,ya yi musu fintinkau a komai._ _A tunanin HAFIZA ta yada ƙwallon mangoro ta huta da ƙuda,sai dai bata sani ba tirka-tirkar da ke cin gidan auranta ya linka wanda ta baro a gidansu sau dubu. Bahagon gida ne mai cike da chakwakiya kala-kala masu matuƙar yawa da ban tsoro. Sai dai faɗin hausawa da suka ce WUYA BATA KISA. Silar zuwan HAFIZA gidan ɓoyayyun sirrikan da ke ɓoye sama da shekara ashirin da biyar sun bayyana a idon duniya. Kar na jaku da yawa🥰 ku biyo tsaftataccen alƙalamina don yi muku jagora zuwa duniyoyi biyun da tunaninku bai je ba🥰_