"Ta kalleshi ta ce, "Abba mai zai hana ka aure ta?"
Ba-zata ya ji maganar, ya qara ware idanuwa yana kallonta, sunanta ya kira kai tsaye,
"Fadimatu, kin san me ki ke fadi kuwa?"
Hawaye ya ciko idanunta, ta ce,
"Halima ita ce wacce mijina yake kiran sunanta cikin bacci, ita ce yake sambatun kiranta in yana kwance da ni. Ita ce yake son cirowa daga qunci ya sanya ta farin ciki, ya fidda ta daga halin da ta ke ciki"
Ta share hawayenta, "Zan taimaka maka don samun kwanciyar hankalina da naka
Wannan sumbato duk a cikin zuciyanta takeyi."
Ku biyoni a wannan murdadaden labari