AL'AJABIN SO

AL'AJABIN SO

  • WpView
    Reads 11,815
  • WpVote
    Votes 81
  • WpPart
    Parts 26
WpMetadataReadComplete Thu, Jan 23, 20254h 49m
Tarihi yana nuna mana abubuwan da suka faru ne kafin mu a rayuwa! Rayuwar duniyar cike take da kalubale, haɗari, wahalhalu da musibu daban-daban, kusan in ka ga ka gujewa hakan to fa alƙalamin ƙaddara bata zana maka ita a shafin ƙaddararka ba, a lokacin da kaddara ke wasa da rayuwarka ya rage maka ɗaukan wannan kalubale a matsayin darasi, ka kuma yi haƙuri da jarabawar Allah (S.W.T) a gare ka. Ni Fatima ban taɓa sanin cewa igiyar ƙaddarar wani na iya shafan na wani har su sarƙe wurin zama abu guda ba sai da na tsinci kaina cikin alkaba'in rayuwa, zafi da kunci suka yawaita a gareni, farin ciki yayi min nisa irin tazarar dake tsakanin sama da ƙasa, na kasa tantance wai ƙaddarar wanene ya shafe ni, shin na mahaifiyata ne ko na mahaifina? Ko kuma nawa ne ni a karan kaina ba'a tsaga ni cikin masu rabauta da duniya ba? A mafi yawancin lokuta in har nayi irin wannan tunani, na kan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sa mana wani tabbataccen al'amari ba, farin ciki ko baƙin ciki yana da lokaci, komai kuma yayi farko to fa yana da karshe, wani karin maganar ma sai ya ce abinda ya baka tsoro a yau babu shakka ko tantama a gobe ya iya baka tausayi, rayuwar tamkar tafiyar hawainiya ce tana tafe tana chanza launi. Al'amuran da suka faru a rayuwata sun sanya min karsashin bayar da labarina.
All Rights Reserved
Join the largest storytelling communityGet personalized story recommendations, save your favourites to your library, and comment and vote to grow your community.
Illustration

You may also like

  • BAKAR WASIKA
  • NI DA ABOKIN BABA NA
  • MY EX CRUSH:MRS ARSLAN ZULKARNAIN HANZ ©
  • KAUTHAR!!
  • KOWA YA GA ZABUWA...
  • FATU A BIRNI (Complete)
  • Waktu Menyimpan Nama Kita
  • SIAPA? |✓|
  • Mutowifku Tersayang
  • MUGUN NUFI!
  • C || TUAH AKALIL : THE BEGINNING
  • ISTERI SANG MAFIA
  • 𝐑𝐚𝐡𝐬𝐢𝐚 𝐓𝐞𝐫𝐚𝐤𝐡𝐢𝐫 𝐑𝐚𝐲𝐪𝐚𝐥 ∆ 𝐂
  • MUNA SON JUNANMU
  • Kaine Rayuwata😭❤❤ Complete
  • Milik Tuan Megat [𝒞 ]
  • NANATOOU (DIYAR KAKA)
  • BAHAGON TUNANI
  • Dr Azeema
  • NADIYA!

BAƘAR WASIƘA... Mai farin rubutu Ban ce tafiyar mai sauki ba ce. Ban muku alkawarin zallar soyayya ba. Ban ce babu farincikin ba. Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki. Labarin Talba, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta... Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira! A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi. Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA... JUANURY 2022

More details
WpActionLinkContent Guidelines