Duk zakaran da Allah ya nufa da cara..... Tafiyar mai tsaho ce, kuma cike take da qalubalen rayuwa iri iri, sanin kanku ne ruwa da Wuta basa haduwa, haka ma haske da duhu dole sai daya ya rinjayi daya, kwatsam sai qaddarar aure ta fada ma USTAX HABIB SAID MAI KAMSHI sannan nen Malamin addini kuma Dr boko, matashi mai kudi,aji da kamala dan gata da ake alfahari dashi a arewacin nigeria, tsakanin sa da ZAINAB HASSAN YAMALTU, bafulatanar qauye, marar ilimin boko da na islama, mara wayewa akan rayuwa marar gata ga kuma tsiwa da taurin kai. Ku biyoni, labarin su ba cike yake da zallar soyyaya ba se dai cike yake da zallar rayuwa ina nufin rayuwa a yanda take, akwai kuka,akwai dariya,samu da rashi,hassada, makirci da soyyaya mai ratsa zukata.