Rayuwa na da wahala a kauyen da al'adi ta fi muhimmanci sama da rayuwar mutanen cikin kauyen. Ko da ace kana da masu sanka a kauyen rayuwa za ta maka wahala ballantana ita da ta taso kowa na mata fatan mutuwa! Mutuwa? To me yasa? Me yasa suke fata mata mutuwa kafin lokacinta ya yi?.
Akwai ciwo a auren da rai ba ya so, ta tsallake matakai masu tsanani da wahala a rayuwarta, daga ƙarshe sai ga shi ta ƙare a auren wanda ba ya sonta, kuma ita ma ba ta sonsa... Auren kiyayya? Wa ya daura shi? Yaya zaman zai kasance?
Akwai ciwo a burin da aka gaza cika shi.
Buri? Fata? Mafarki? Su ne abubuwan da a ko da yaushe sai ya yi mafarkin samunsu, amma har kawo yanzu burin nasa ya gaza cika, wani irin buri ne wannan da cikarsa ta zamewa mai shi alaƙaƙai?.
Fansa ita ce abin da yake kwanta yake tashi da ita a ransa. Fansa? Wace fansa ce wannan? Me akai masa da yake son sai ya rama?
Kowa a garinsu kallon ganga ba rufi yake mata, don me? Saboda kawai ana ganin cewa ba a san asalinta ba, ba wannan kaɗai ba, ba aje ko ina ba wata jarrabawar da ta fi wannan ta faɗo mata, jarrabawa? Wace irin jarrabawa ce wannan?
Find out in ƘAWA ZUCI (The beautiful game of love and revenge).