Mutum ne shi Mai girman Kai, Amman zuciyarsa cike take da boyayyen ciwo. Ita kuma mace ce Mai hakuri da Sanin ya kamata, Amma itama nata zuciyar dauke take da raunuka da suka bar mata tabbai. A zuciyar kawarta kuwa, wani buri ne boye da zai iya lalata komai. A lokuta da dama idan girman Kai ya hadu da hakuri, zukata kan iya karyewa, sirrika zasu tonu, soyayya Kuma zata fuskanci jarabawar da bazata taba mantawa da ita ba. Ku biyo ni cikin duniyar Fuad Smith, inda ko wace zuciya ke dauke da wani sirri. Written in Hausa.
Daha fazla bilgi