22 parts Ongoing Zara-zaran yatsun hannunta wanda suke sanye da zobina masu matukar kyan gaske da d'aukar hankali ,idona ya soma hangowa sanadiyyar motsa hannun da take tana juya stearing tana ɗan kad'asu lokaci-lokaci saboda wak'ar dake tashi a cikin Motar, tare da fitar sautin siriryar muryarta me dadin saurara.
'I don't care who you are, where you from what you did as long as you love me'. sautin dake tashi kenan a cikin motar na Back Street Boys wanda take marming kamar ita tayi shi.
yayinda a hankali take motsa lips dinta kamar batason motsasu, gefe guda kuma zuciyarta ke bugawa da matsanancin karfin gaske wanda ta rasa dalili faruwar haka tun safe ta tsinci kanta cikin tsanani faduwar gaba ..