*" Na ji ana faɗin Mutuwa hutu ce gurin Mumini,tabbas ina son Mutuwa so na haƙiƙa! Amma kuma ina tsoronta fiye da komai ciki da waje na.Ina son Mutuwa saboda na ƴantu daga azabtuwar ruhi wadda ba ta yankewa tsakanin dare ko rana,ina kuma tsoron Mutuwa ne saboda ni da kaina banwa kaina shaidar zama cikin Muminai ba! Ban jin Allah zai dubeni da idon rahamarsa saboda tarin ZUNUBI NA da yawanshi ya fi kumfar koguna iya sanin mai karatu,na tuba daga laifuka na! Haka kuma na kasa barin laifukana ina gudunsu suna sake kusanta ta...Tabbas sai na Mutu,lallai kuma ina son Rayuwa,ga tururin ZUNUBI NA yamin ƙunar da zata zama AJALI NA! Ina mafita?"*