GAWA TAFE. Zombies story sun shiga wata masifa ta rayuwa a sadda basu yi tsammani ko tunanin riskarta ba. Sun taso Yara ne masu gata, sun samu duniya da abunda ke cikinta. Su taka kowa ba wani abu bane a wajansu, an sangartasu da naira dukiya suna bashashar duniya. Sai dai suna cikin jin dad'in duniyar zata juya masu baya tayi juyin gwado dasu, a inda basu tab'a tsammani ko hasashen akwai irin masifar ba a duniya, sai gashi ta riske su a inda basu da kowa, basu da Mai kawo masu d'auki bare ya k'are su daga Mutuwa...........