A tunanin Rumana ta gama tsara komi na rayuwarta tun bayan da ta fara aiki a national hospital Abuja, sannan ga alkawarin soyayya tsakanin ta da masoyinta tun tana jami'a watau Engineer Mu'azzam da ke haɗa PhD dinsa a Berlin, ta gama tsara yanda mafarkinta zai cika, ta tsara yanda za ta daidaita aikinta, soyayyarta da iyalinta. Kwatsam, sai Mu'azzam ya ɓace kamar wanda ya taɓa layar zana, nan ya barta da tarin tambayoyi a zuciyarta, ya barta da miƙi, ya dawo mata da hannun agogo farko. A lokacin da take ganin ta gine bangon da ya faɗi, sai kuma Dr. Marzuq ya shigo rayuwarta ta dalilin ciwon mahaifinta. A hankali shaƙuwa ya yi karfi tsakaninsu a matsayinsu na ma'aikatan lafiya kafin Dr. Marzuq din ya bijiro mata da zancen soyayya, har aka sanya rana, aka kawo lehe kafin tarihi ya maimaita kansa. A nan ta fahimci kuskuren da ta tafka, kuskuren da ya sa Mu'azzam ya barta shi ya sa mahaifiyar Marzuq ta hana auren. Kuskure ne da al'umma su ka ɗaura mata ba wai ta aikata shi ne da gangan ba. Ba Ta gama farfadowa daga kuncin rabuwa da Marzuq ba wani ɗan kasuwa ya mata tayin rayuwa wanda ya bambam da na Mu'azzam da Marzuq. Nan ta shi ga rudani, tsakanin kurwan soyayyarta na farko, ko kwalelen soyayyar likita da amince ma zama mata ta uku a gidan Alhaji Musa. DISENCHANTMENT ( Labarin Rumana) Labari ne da ya kunshi soyayya, karatu da aiki a wajen ƴa mace; musamman wacce ta haura shekaru 30 bata yi aure ba. Kallon da ake mata da kuma yanda ake yanke mata hukunci a kan laifin da bata aikata ba. Ana so tayi aure amma an ƙi a bari a aureta.All Rights Reserved
1 part