DAHUWAR ƘAHO

DAHUWAR ƘAHO

  • WpView
    MGA BUMASA 1,255
  • WpVote
    Mga Boto 5
  • WpPart
    Mga Parte 15
WpMetadataReadOngoing3h 39m
WpMetadataNoticeHuling na-publish Tue, Jun 17, 2025
WpInfo
Fiction
Romance
Ni da ku mun san, zamani rikiɗa yake tamkar hawainiya. Kowanne zamani da suffar da yake tafiyar da al'ummar cikinsa. A wannan zamanin na tafiyar biri a yashi, wasu matan sukan kalli ƙarin aure ta munanan fuskoki. Musamman yadda iyayen gida suke ganin wayonsu ne, yasa aka auro su a matsayin iyayen gida. Har wasu suke cin duniyarsu da tsinken tsire, ta hanyar gasawa amare gyaɗa a hannu. Su ɗanɗanawa maza kuɗarsu don hana su rawar gaban hantsi. Saboda suna ganin sun zama kujerun gida, dole a zauna da su.Ba tare da sun hangi me gobensu zata haifar ba. Duk yadda ake ganin iyayen gida suna juyin waina da amare,lamarin bai sauya zani ba. Domin ɓagaren amaren da suke cin alwashin mijin wata ne zaɓinsu, a guntun tunanin wasu. Suna tsammanin gazawar uwargida ne yake sa miji aurensu. Musamman wasu mazan, da suke kwayewa uwargida baya tun a neman aure. Silar haka amare suke hangen kansu a bigiren cusgunawa uwargida, don su nuna mata miji ya daina yayinta. Batare sun hangi yankan kunkurin-Balan da suke wa rayuwarsu ba.
All Rights Reserved
#11
zafafabiyar
WpChevronRight
Sumali sa pinakamalaking komunidad ng pagkukuwentoMakakuha ng personalized na mga rekomendasyon ng kuwento, i-save ang iyong mga paborito sa iyong library, at magkomento at bumoto para lumago ang iyong komunidad.
Illustration

Magugustuhan mo rin ang

  • KWANTAN ƁAUNA
  • Bin Son Zuciya
  • KAICO NAH
  • 𝐔𝐒𝐓𝐀𝐙 𝐃𝐀𝐘𝐘𝐀𝐍 𝐙𝐈𝐐𝐑𝐈
  • MAI ƊAKI...!
  • BAYA DA ƘURA
  • KAUTHAR!!
  • NADIYA!
  • BA NI DA IKO...

Izza, mulki, ƙasaita sun tattara a gare ta ita kaɗai. ƴar sarki ce, jikar sarki ce, matar sarki ce. Bata ƙaunar talaka, bata son haɗa hanya da talauci. Burinta ɗaya tak ya rage a duniya; shi ne ɗanta ya zama sarki, ita kuma ta zama babar sarki kuma kakar sarki na gobe. Sai dai kash! ƴaƴan nata maza har guda uku, masu matuƙar kama da juna, sun kasance babu wanda yake da qualities ɗin riƙe ragamar al'umma. A Lokacin da burinta ke gab da cika kwatsam aka ti mata dirar mikiya, ƴar talakawa, baƙa, gurguwa, mai tallan abinci ta shigo rayuwar samarin ƴaƴan nata guda uku, gurgurwar da ta zama silar girgizar duniyarta da burinta, gurgurwar da ta haddasa mata raunin da bata da shi, gurguwar da ta zamar mata inuwar dodo, gurguwar da ta zama mata ƙadangaren bakin tulu. Shin me zai faru? Ta wacce hanya gurguwa zata kutso cikin rayuwar waɗannan jinin sarautar...? Waye zai zama sarki cikinsu ukun duk da kasnacewar su masu kama ɗaya? ina alwashin da ta ɗauka na ganin cewar sai taga bayan duk wanda ya nemi ya ruguza lissafinta?, ina alwashinta na cewar sai ta kassara rayuwar wanda ya kawo kutsen hana ɗanta zama sarkin gari....?

Karagdagang detalye
WpActionLinkMga Alituntunin ng Nilalaman