A duniyar mayu, Duniyar da gamagarin mutane basu da 'yanci,
duniyar da ɗan adam ke da ikon sarrafa kwayoyin zarra,
Duniyar da masu karfi ke yin irin rayuwar da suka so.
duniyar da masana lissafin taurari da masu ilimin fasaha da sanin sirrin numfashi kaɗai ke da daraja.
To akwai wani yaro da ya tashi cikin maraici, sai dai shi wannan yaro bashi da ikon sarrafa wani abu da ya shafi ikon zarra, fasaha ko numfashi.
Saboda haka cikin ƙwārin gwiwa ya ɗauki takobi da niyyar ya shāfe duk wani maɗaukaki a wannan duniya.
wannan saurayi sunansa
BARHAM