Hannu na karkarwa yake, jiki na har bari yake, saboda tun da nake Rai na Bai taba baci ba kamar yau, ban taba tunanin Baba zai iya abin da yayi yau ba, na saka hannu na na toshe kunne na saboda na daina Jin muryar shi, Amma tamkar a gaba na yake ihun, tamkar ni din yake yiwa masifa
"...Saboda ke Baki da mutunci, ke ba yar mutunci bace ba, har ni zance kiyi Abu ki kiyi, to se de ki bar min gida na yau dinnan, ki fito ki hada kayan ki ki bar min gida na, ni ba shashan namiji bane ba..."
He kept on saying, ya cigaba da fada Yana yarfa zagi, na zata zagi na Yan kauye ne, na zata ana yin zagi ne ga mutanen da ba su da ilimi, se gashi Baba ne yake zagin Mama a tsakar gida, a gaban mu, gaban kishiyar ta, gaban almajirai, masu aiki yake mata wannan cin mutuncin, nasan ya taba, ba sau daya ba, ba sau biyu ba Amma Bai taba cin mata mutunci irin na yau ba, a gani na ko Babu komai ya kamata taci albarkacin mu, ya kamata ya daga mata kafa saboda mu, se naji zuciya ta tana zafi, tana zugi na kasa hakuri na fito daga dakin, Kai a lokacin ma it's as though I'm possessed saboda wallahi kwakwalwa ta bata tare da ni, zuciya ta ce kawai ke fada min kada na bari, kada nayi shiru cin mutuncin yayi yawa, na kuwa fito tsakar gidan, gidan yayi tsit saboda Baba ya gama ya wuce dakin shi, se almajiran mu biyu suna yiwa Amarya shanyar labule da suka wanke mata, na wuce su na nufi dakin shi fuska ta tayi Wani irin ja, hatta wata vein da nake da ita a goshi na ta fito, tabbacin Rai na ya baci, Yana zaune na same shi a parlon shi, na kalle shi saboda ko sallama banyi ba shi ma ya kalle ni nace
"Baba! Me yasa zaka dinga cin zarafin Maman mu a gaban mu, a gaban kowa a gidannan, me tayi maka?"
Se ya dago ya kalle ni, I can see the amazement in his eyes, saboda yayi mamaki, baiyi tunanin bakar zuciya ta har ta Kai haka ba...
Inaaya
Rayuwa mai ɗauke da ƙunci da kuma tarin baƙin ciki, Yayinda hasken wata ke fitowa yana haskaka samaniya, a lokacin ne kuma zuciya keyin zafi da wani irin tafarfasa, Idaniya sun makance dalilin zubar Hawayen da ban san yaushe ne zai tsaya ba, Ina jin inama zan iya kashe kai na! Ko hakan zai sanya zuciyata ta samu nutsuwa da kuma salama, a lokacin da kowa ya kamata yayi farin ciki a lokacin na kejin duniya nayi min zafi, Idaniyan zuciyata na tafarfasa, ban sani ko zan zama dai-dai kamar kowa? Ban san yaushe rayuwa zata juya min daga juyin wainar fulawan da take dani ba, rayuwata ita ake kira da GABA GAƊI rayuwa mara ƴan ci, ko wacce mace na amsa sunanta dana mahaifinta yayinda ya kasance ni kuma ina amsa sunana kana na bashi makari da TSINTACCIYA!