Taƙaitaccen labari: Labarin Rahma. Marainiyar yarinya wacce ta taso da sha'awar talla a rayuwar ta. Wanda hakan ya kai ta ga halaka saboda rashin biyayya ga mahaifiyarta, biyewa shawarwarin gurɓatattun ƙawaye, kwaɗayi da son abin duniya. Sannan a ƙarshe rayuwar ta ya lalace. Littafi ne dake magana a kan rashin neman ilmi na boko da na addini, rashin neman sana'a mai kyau. Littafi ne dake faɗakarwa a kan yaki da jahilci da kuma neman sana'a domin dogaro da kai.
Ubangiji Allah ya bamu ikon isar da saƙon da ke cikin wannan ɗan ƙaramin littafin.