14 parts Ongoing A tsakanin duniya biyu mabanbanta, ƙaddara ta yi kutse a tsakanin rayuka biyu. Duk a ƙarƙashin kalma ɗaya:
"soyayyah!"
Tunaninta da duk wata nutsuwarta sun karkata ne akan sama masa mafita da ga duhun ƙaddarar da ya yi masa ƙawanya, sai dai, da ga baya ta yi realizing cewa ta faɗa a tarkon son sa, soyayya mai tsanani ga Yusuf Hateym Al'qasrawi.
kyakkyawan balarabe ma'abocin Addinin musulunci, saɓanin ita da ta kasance krista wadda bata gasgata kaɗaituwa Ubangiji mahalicci ba.
Abu ne mai matiƙar wahala ta iya mallakar zuciyar Yusuf wadda ya jima da mallakawa Matarsa Yumnah Sulaiman El'ghanee, kyakkyawar Balarabiya mai kwarjinin musulunci.
Doctor Chioma Nonso Chukuma, ta Fahimci ba zata iya karawa da Yumnah Sulaiman a zuciyar Abu'hateym ba, wannan ya sa ta ƙara ƙaimi domin yaƙi akan ƙudurinta. Musamman data fahimci babu gurbi da ya yi saura, wanda Yusuf ke jin zai iya mallakawa wata ɗiya mace a duniya...!
08102777485