Ilham ta taso cikin ƙuncin rayuwa, tana yin tallah da zuwa makaranta cikin wahala. Duk da haka, burinta na ilimi bai mutu ba - duk da cewa kudin jarabawa da sauran ƙalubale suna barazanar hana ta cimma mafarkinta.
A gefe guda kuma, lokaci yana tafiya. Shekarunta suna ƙaruwa, tana ji daga bakin jama'a: "Kin kai shekaru, kina nan ba aure ba..." Wannan kalma tana ɗaure mata zuciya, tana jefa ta cikin addu'ar samun miji nagari daga Allah.
Rayuwa, ilimi, soyayya, da addu'a suna haɗuwa a cikin tafiyar Ilham.
Shin za ta cimma burinta? Za ta iya tserewa matsin lamba na aure? Kuma wane irin ƙaddara ce take jiranta?