Story cover for MATAR SADAM  by pen_of_simplicity
MATAR SADAM
  • WpView
    Reads 148
  • WpVote
    Votes 5
  • WpPart
    Parts 9
  • WpHistory
    Time 2h 26m
  • WpView
    Reads 148
  • WpVote
    Votes 5
  • WpPart
    Parts 9
  • WpHistory
    Time 2h 26m
Ongoing, First published Sep 06
2 new parts
littafin matar sadam littafi ne da ke kunshe da abubuwa da dama kama daga Kan ribar biyayya wa iyaye, zamantakewar aure, makirci, soyayya, kishi, zagon kasa D.D.S Ku dai kawai Ku biyo alqalamin young writer Dan ganin yadda zata Kaya



TSOKACI



Baya tayi da sauri tana dora hannun ta a baki ba tare data lura da magen dake kwance a wajen ba tayi baya da sauri kara magen tayi wanda ya sata buga tsalle ganin ta take mata jela .
Tsallen da tayi yasa takalmin ta yin kara da sauri ta cire takalmi tayi kasa da gudu .

 motsin da umma taji ne ya sata cewa wadda take wayar da ita " ina zuwa hajiya haleema tsaya karki kashe.........



*****wayar sa dake Kan table din ce ta dauki ruri ko kallon ta baiyi ba balle asa ran zai dauka, kusan missed calls 6 ganin anki daina Kiran yasa shi daukan wayar Yana jan tsaki , sunan seena ya gani Yana yawo kan screen din wayar zubawa wayar Ido yayi kamar bazai dauka ba sai kuma wani tunani yazo masa gaban sa ne ya fadi cikin sauri yayi picking tare da Karawa a kunne muryar sa har sarkewa take wurin fadin he..........
All Rights Reserved
Sign up to add MATAR SADAM to your library and receive updates
or
#13hausa
Content Guidelines
You may also like
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
18 parts Complete
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
61 parts Complete
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
You may also like
Slide 1 of 10
မောင့်ဒေး ရဲ့အချစ်ကလေးဖြစ်ချင်တယ်(Completed) cover
KALLON KITSE cover
DUK A SANADIN SOYAYA cover
 𝑻𝒂𝒏𝒉𝒂𝒊: 𝑻𝒉𝒆 𝒔𝒂𝒈𝒂 𝒐𝒇 𝑨𝒍𝒊'𝒔 cover
FATU A BIRNI (Complete) cover
RAYUWAR BADIYYA ✅  cover
EMAAN cover
BAKAR WASIKA cover
MATAR AMEER cover
ဆိုင်သူ့နှလုံးသား cover

မောင့်ဒေး ရဲ့အချစ်ကလေးဖြစ်ချင်တယ်(Completed)

78 parts Ongoing

📌ဤဇာတ်လမ်းသည်စိတ်ကူးယဥ်ဇာတ်လမ်းဖြစ်တဲ့အတွက်လက်တွေ့ဘ၀နဲ့ကွာခြားပါလိမ့်မယ်။ "မဟာထိုက်တန်+စောအယ်ဒေး"