"Haka nake yawo, bana saka talkami." Ahankali, Nazir ya durkusa, guiyoyinsa suka baje kasa. Ya kai hannunsa ya rike kafar Batula, sannan ya dago idanunsa cikin natsuwa kamar mai rokon afuwa ya kalleta. Ganin za ta zame yasa ta rike kofar. Ya sunkuyar da kansa ya sumbaci tafin kafarta a gaban kowa. Batula ta bude idanunta da suka cika da razana, zuciyarta na dukan kirjinta tamkar gangar yaki. Tsoro da kunya suka hadu. Nazir ya sauke kafar, ya kama hannunta tamkar wanda ya yi nasara a yaki, ya ja ta cikin falon ba tare da jin kunya ba, daman fargaba da tsoro ba halinsa ba ne. Sai falon ya dauki shiru. Ko amo na numfashi babu, kowa ya kasa motsi. Idanuwa suka manne kansu tsabar mamaki, duniyarsu ta tsaya cak tana jiran abin da zai biyo baya. *** *** *** Mafi yawanci saba ji da ganin mace sai ta yi hawaye kafin ta samu farin ciki. Amma "Gumbar Dutse" Zai nuna muku wata hanya dabam inda soyayya ta zama ruwan sanyi, aure ya zama gata, kuma mace ta sami damar rayuwa cikin aminci da kauna har sau biyu a rayuwarta. Duniya ta yi ma Nasreen dadi. Ko kun san akwai mazan da basa juyawa mace baya, akwai masu rikon Amana gina rayuwar iyalinsu? Soyayya ba wai mafarki ba ce gaskiya ce idan aka hadu da nagari. Labarin Batula, Nasreen, Nazir, da kuma Zayyan.All Rights Reserved
1 part