Story cover for BA NI DA IKO... by FareedaAbdallah
BA NI DA IKO...
  • WpView
    Reads 99
  • WpVote
    Votes 10
  • WpPart
    Parts 9
  • WpHistory
    Time 1h 48m
  • WpView
    Reads 99
  • WpVote
    Votes 10
  • WpPart
    Parts 9
  • WpHistory
    Time 1h 48m
Ongoing, First published Oct 02
🖤 BA NI DA IKO...

Rayuwa ta ɗauke ta zuwa wani wuri da ko a mugun mafarki bata taɓa tsammani ba.
A hannunta akwai sarƙa, a zuciyarta akwai raɗaɗi, a idanunta akwai hawaye.

Ta yi ƙoƙarin gudu daga ƙaddara, amma ƙaddarar ta riga ta fi ƙarfinta.
Ta so ta yi ihu, amma muryarta ta mutu tun kafin sautin ihun ya fita.
Ta so ta yi zaɓi, amma ƙaddara bai bata damar yin hakan ba...

Ita mace ce ƴar shekara goma sha bakwai, amma tun daga yarintarta ƙaddara ta jefa ta cikin duhu mai tsanani...
A lokacin tafiya cikin wannan duhu ne ta fahimci gaskiyar kalmar:
"Ƙaddara ba ta tambaya ko kana da iko ko babu, sai dai ta tilasta maka yin abin da take so..."

©Fareeda Abdallah
*Littafin kuɗi ne, akan farashin 1k kacal. Masu niyyar siya za su tura kuɗi a cikin wannan account ɗin 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 07039080978 Domin samun damar shiga group ɗin da za'a dinga posting a Telegram.*
All Rights Reserved
Sign up to add BA NI DA IKO... to your library and receive updates
or
Content Guidelines
You may also like
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
61 parts Complete
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
You may also like
Slide 1 of 10
SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅) cover
SIRRIN MU cover
Komai  Tsananin Duhu.... (ON GOING) cover
KOWA YA GA ZABUWA... cover
KWANTAN ƁAUNA cover
BAKAR WASIKA cover
The Coldest Warmth cover
NAMIJIN GORO... cover
RAYUWAR BADIYYA ✅  cover
Tsohuwar Soyayya (Best Hausa love story) cover

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)

20 parts Complete

Who doesn't love a short love story? 💕 Labarin ruguntsumin masarauta mai dauke da soyayya! Ya zata kaya ne ga Yareemah Aliyu wanda ya dauki son ransa zai aura iyayen sa suka tilasta masa auren yar uwar sa Meenah! Bayan ga basma SON RAN SA? Meenah kuma ZABIN IYAYEN SA CE! Ya zaman nasu zai kasance? Shin nagaya muku MEENAH yarinya ce karama? Being deeply loved by someone gives you strength, while loving someone deeply gives you courage.MEENAH da YAREEMAH ALIYU