ILHAM-------PART TWO
Rayuwa ta fara ɗaukar sabon salo.
Bayan dukkan ƙoƙari, addu'a, da hawaye, Ilham ta fara jin kamar zuciyarta tana buɗe wani sabon shafi - shafi da ba ta san me yake cikinsa ba.
Wasu mutane zasu shigo rayuwarta kamar haske, wasu kuma kamar inuwa.
Amma kowanne daga cikinsu zai ɗan motsa wani sashi na ƙaddarar da take boye a gaba.
A cikin ruɗanin rayuwa, Ilham zata ci gaba da neman amsar tambayar da ta dade tana yiwa kanta:
"Shin lokaci ne bai yi ba, ko kuwa ni ce ban gane lokacin ba?"
Wannan sabon bangare, ba kawai labari ba ne - tafiya ce ta zuciya, imani, da gano ma'anar jarumtar mace.
"Kaddara bata taba jinkiri - sai dai mu ne muke kasa gane lokacin zuwanta."